BBC News Hausa (@bbchausa) header
BBC News Hausa (@bbchausa) profile picture

BBC Hausa - Fiye da shekara 60 na labaran duniya da rahotannin da suka shafi rayuwarku

London
Joined December 2008
Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)Photo by BBC News Hausa (@bbchausa)
Iyalan masu haƙar ma'adanai 33 da suka rasu a hannun jami'an hukumar NSCDC a jihar Neja, sun ce sun yi farin ciki da shawarar da kwamitin binciken ya bayar na biyansu diyyar naira biliyan 1.4. Kwamitin ya gano cewa mutanen sun mutu ne sakamakon cunkoso da tsananin zafi.
6
32
7,687
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, wanda ya zo daidai da cikarsa kwana 256 a tsare, El-Rufai ya ce yana da haƙƙin samun shari’a ta gaskiya da adalci. Ƙarin bayani - bbc.in/3WEMEPE
16
39
2
448
13,815
Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a garin Bitta da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno, da kuma Buni Yadi da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe, a daren ranar 29 ga Oktoba zuwa safiyar 30 ga Oktoba, 2026. Ƙarin bayani - bbc.in/4BARWfc
3
10
2
63
6,592
Shugaban ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala ibadun, inda ya bayyana Umrah a matsayin wata gagarumar ibada da kuma damar yin addu’a ga Najeriya. Ƙarin bayani - bbc.in/48ljzvg
5
9
2
132
8,204
Hukumar zaɓen Najeriya INEC, ta fitar da sanarwa kan sunayen ‘yan takarar da ta ce za ta mayar da su amma ba ta bayyana su wane ne kuma yaushe za ta yi hakan ba. Mece ce makomar takarar Farfesa Pantami da Comrade Gwarzo da na Kano? #pantami #inec #gwarzo #ndc #pdp #gombe #kano
4
7
1
80
8,813
Pantami da Gwarzo na daga cikin sunayen ƴantakarar gwamna da suka ɗauki hankali, bayan da a karon farko INEC ta cire sunayensu dage jerin ƴantakara Ƙarin bayani - bbc.in/4surUWI
11
155
11,178
Sakamakon ƙarshe na zaɓen 'yan majalisar dokokin Isra'ila ya tabbatar cewa ƙawancen jam'iyyun Benjamin Netanyahu ya lashe kujeru mafi yawa, amma ya gaza samun rinjayen da ake buƙata. Ƙarin bayani - bbc.in/3W1BuV7
2
13
1
154
12,053
An samu ƙaruwar muhawara a Arewacin Najeriya kan ƙungiyoyin da ake kira ƴan Qur'aniyyun ko Qur'ani zalla, wato mutanen da suke da ra'ayin cewa Alƙur'ani kaɗai ya isa a matsayin tushen addinin Musulunci ba tare da komawa ga Hadisan Manzon Allah (SAW) da tsarin fikihun malamai ba.
11
14
1
144
11,480
Fitowar aƙidar Qur'ani zalla a Arewacin Najeriya na wakiltar wani muhimmin sauyi a tunanin addinin Musulunci, domin yana ƙalubalantar tsarin ilimin Musulunci da aka gina tun ƙarni da ƙarnuka. Ƙarin bayani - bbc.in/4ipR44h
9
7
104
6,059
Hotuna da rahotanni daga cikin makarantu a Iran sun nuna ana koyar da ɗalibai yadda ake amfani da makamai, lamarin da ya haifar da tambayoyi game da ƙaruwar katsalandan ɗin hukumomin soji da na tsaro a cikin makarantu. Ƙarin bayani - bbc.in/4kqaKaF
6
5
135
5,584
A yayin da shirye-shiryen ƴanhamayyar Najeriya na dunƙulewa wuri ɗaya don tunkarar Tinubu a zaɓen 2027 ke fuskantar koma-baya, wasu ƴanƙasar sun fara tunanin ko ƴan adawar za su iya kai labari a zaɓen mai zuwa. Ƙarin bayani - bbc.in/4ieKjDx
2
1
61
5,001
Trent Alexander-Arnold na iya zama ɗan wasan da Chelsea za ta yi zawarci,, yayin da Manchester United ke duba yiwuwar ɗaukar dan wasan gaba na Leeds United, Dominic Calvert-Lewin. Ƙarin bayani - bbc.in/4A64R7q
2
65
3,895
Yadda Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauka a Jeddah gabanin gudanar da ibadar Umrah a Makkah. Tinubu ya samu tarba daga Abdulaziz Yari da Abdussamad Rabiu da sauran ƴan Najeriya da jamiʼan Saudiyya. Tace hoto - Aminu Kutama
6
14
152
16,467
Tinubu ya tafi Saudiyya domin aikin Umara Ƙarin bayani - bbc.in/4zSqAPO
3
7
64
9,021
Soyayya ruwan zuma 💝 Wata matashiya ce soyayya ta ɗibe ta, ta haye saman hasumiyar sabis, kuma ta ce ba za ta sauko ba sai iyayenta sun ɗaura mata aure da saurayin da take so. Za ku iya wannan kasadar domin soyayya? #india #mumbai #soyayya #love
5
19
128
19,148
A rana irin ta yau, 29 ga watan Oktoba, shekara 20 ke nan da rasuwar marigayi Sarkin Musulmi na 19 a Najeriya, Alhaji Muhammadu Maccido, a wani hatsarin jirgin sama a shekarar 2006. Ƙarin bayani - bbc.in/4BA5hnZ
12
22
1
305
10,725
Shin me ya sa Tinubu ke ta ɓullo da sabbin tsare-tsaren rage raɗaɗi ga 'yan Najeriya? A baya-bayan nan, gwamnati ta gabatar da shirin bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin 70,000 duk wata har tsawon wata shida, makonni bayan ta fitar da shirin tallafin rage farashin man fetur.
10
6
108
12,006
Nan gaba a yau ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC za ta fitar da matsaya kan wasu ƴantakarar gwamna da ta cire sunayensu daga cikin jerin ƴantakara a zaɓen 2027 da ke tafe. Karain bayani - bbc.in/4e6kenF
4
14
1
271
18,673
A yayin da ake ci gaba da ƙirga ƙuri’un zaɓen, Jam’iyyar Likud ta Firaminista Netanyahu, ta zargi jam’iyyun Larabawan ƙasar da maguɗin zaɓe ta hanyar cin hanci da razanarwa da amfani da tashin hankali. Ƙarin bayani - bbc.in/3Umf0O2
3
7
1
85
9,482
Kun san ana sayar da tsire da sauran abincin Hausawa a birnin London? Umar Bala, ɗan asalin Kano, ya bayyana yadda ya yi nasarar bunƙasa sana’ar sayar da abincin Hausawa a Ingila, inda ya fara a cikin ƙaramar mota har ta kai ga buɗe gidan abinci. 🎥 - Muhammadu Buhari Fagge
5
21
191
11,907